A yau a shirin mu na nishadi dandali ya samu bakwanci mawaki Muhammad Kabir M K Na-kudu wanda ya fara waka tun shekara ta 1996 a lokacin yana makarantar sakadare bayan sun je wata makarantar yan mata a garin Madobi domin gudanar da gasar makaranta inda wata daliba ta rubuto masa wasikar cewar ta na son sa.
Wannan ne ma ya bashi kaimin tsunduma harkar waka inda ya rubuta mata waka a wancan lokaci, ya kuma ce yana samun nishadi a lokacin da yake rubuta waka.
MK Na-kudu dai ya ce yana harkar waka ne domin nishadi domin kuwa yana da sana’arsa a lokaci guda kuma yana isar da sako ga alumma.
Ko da ya ke ya fi maida hankali wajen wakokin soyayya, yanayin tarbiyayya da harkoki na yau da kullum.
A fannin tsegumi kuwa kamfanin JAGA WORLD sun dawo cigaba da aikin film din Malam Zalimu a garin Kano.
A cigaban shirin dai an sanya Sule Bosho ya maye gurben marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.
Ko biyo mu domin cigaban shirin.