Shugaban hukumar kwallon kafar Italiya Carlo Tevecchio ya bayyana cewa hukumar sa na shirye da ta fara tattaunawa kan sabunta kwantaragin koch Antonio Conte.
A kakar shekarar da ta wuce ne koch din mai shekaru 46 da haihuwa ya fara jagorantar kungiyar wasan ta Azzurri, wanda ya gaji tsohon koch Cesare Prandelli, bayan da yayi murabus biyo bayan cire kasar da akayi a wasan cin kofin duniya.
Antoni Conte dai shine ya jagoranci kungiyar Jeventus har ta samu zakaran wasannin Serie A har sau uku, kafin ya karbi jagorancin kungiyar wasan ta kasa, wanda a yanzu haka yake ka har sai bayan wasannin gasar cin kofin Turai ta shekara ta 2016 kafin karshen kwantiraginsa, amma shugaban hukumar kwallon na shirye domin ganin an sabunta kwantiragin kocin .
A lokacin da manema labarai ke yiwa shugaban hukumar kwallon tambaya, ya bayyana cewa Koch Conte, koch ne mai sanin aikin sa da bai taba ganin irin sa ba, ya kuma ce idan ka tambayeni, a shirye nake da na sabunta kwantaraginsa, kasancewar ya cika duk abinda ake bukata har ma dana masu ‘daukar nauyin kungiyar mu wato Puma.