Hukumar da ke kula da kwallon kafa ta nahiyar Turai ta fitar da jaddawalin, rukunin kungiyoyin da zasu fafata a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, UEFA champions league, na shekara 2017/18.
Kungiyoyi talatin da biyu da suka fito daga kasashen Turai zasu gwabza a tsakaninsu domin fidda zakara a tsakani.
A shekarar da ta gabata na 2016/17 kungiyar Real Madrid, na kasar Spain, ita ta lashe a karo na goma sha biyu,
Wannan fitar da jaddawalin, ya gudana ne a Monaco, kasar Faransa,
bisa tsarin kowa ne rukuni nada kungiyoyi hudu a ciki an kuma kasafta kungiyoyin ne har gida takwas.,
A rukunin (A) a kwai Benfica, Man United, FC Basel, CSKA Moscow,
Rukunin (B) Bayern Munich, PSG, Anderlecht, Celtic,
Rukunin (C) Chelsea, Atl Madrid, AS Roma, Qarabag,
Rukunin (D) Juventus, Barcelona, Sporting CP, Olympiacos,
Sauran rukunin kuwa sun hada da rukunin, (E) wanda ya kunshi, Spartak Moscow, Sevilla, Liverpool,
Maribor, Rukunin (F) Shakhtar Donest, Man City, Napoli, Feyenoord, Rukunin (G) AS Monaco, FC Porto, Besiktas, RB Leipzig, Sai rukunin karshe na (H) Real Madrid,B Dortmund,Tottenham,. Apoel, Za'a fara wasanninne a watan tara na shekara 2017.
Your browser doesn’t support HTML5