Jaddawalin Wasannin Share Fagen Cin Kofin Duniya

A cigaba da wasannin sada zumunta da ake yi tsakanin kasa da kasa domin shirye shiryen tunkarar gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a watan yuni 2018 a can kasar Rasha.

A jiya kasar Brazil ta doke Croatia daci 2-1

Albania 1-4 Ukraine,

Costa Rica, ta lallasa Northern Ireland daci 3-0

Spain nada 1 Switzerland 1,

Mexico 1-0 Scotland,

Saudi Arabia ta sha kashi daci 3-0 a hannun Peru.

A yau kuma kasar India zasu fafata da kasar Kenya, Armenia da Moldova, Serbia da Chile, Morocco zasu barje gumi da Slovakia, sai kuma kasar Itali su kara da kasar Malta.

Za a fara wasannin ne tun daga misalin karfe 3 da rabi na yammaci har zuwa takwas saura kwata na yamma agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Kenya Ghana.

Your browser doesn’t support HTML5

Jaddawalin Wasannin Share Fagen Cin Kofin Duniya