Jama'atu Nasril Islam Ta Ce Ba A Kyautawa Musulmin Najeriya Ba; An Fasa Gungun Cinikin Jarirai A Ogun; Ebola Ta Bulla A Guinea; Kwararru Sun Ce Jirgin Malaysia Ya Fada Cikin Teku Ne - 24/3/2014

Litinin 24/3/2014
NAJERIYA - ABUJA - A yau litinin aka koma zauren taro na kasa a Najeriya inda wasu wakilan ke kushe wannan taro, abinda ya sa wani dan majalisa yace duk wakilin dake kushe taron, ya fita daga ciki mana. Kungiyar al’ummar Musulmin Najeriya, Jama'atu Nasril Islam, ta bakin sakatarenta, Dr. Khalid Aliyu Abubakar, ta bayyana yadda aka zabi wakilan taron a zaman na son zuciya. Wasu masu fashin baki irinsu Solomon Dalung, sun soki yadda ba a sanya matasa a cikin taron ba.

NAJERIYA - OGUN - ‘Yan sanda a Jihar Ogun ta Najeriya sun fasa wani garken masu yin ciki ma ‘yan mata su na sayar da jariransu. Kwamishinan ‘yan sandan na jighar Ogun ya fadawa wakilinmu cewa sun damke matar da aka samu tana kula da wadannan ‘yan mata masu ciki. Wannan sana’a dai an fara tono ta a Jihar Abia, shekaru da dama da suka shige, inda aka yi ta samun wurare da dama da ake ajiye mata masu juna, idan sun haihu sai a kwace jariran nasu domin a sayar wa da masu neman haihuwa ba su samu ba, ko kuma dai wasu mutanen masu mummunar akida ta yin amfani da jariran wajen wasu ayyukan tsafi.

AFIRKA - GUINEA - Jami’an kiwon lafiya sun ce annobar zazzabi mai sanya tsiyayar jini dake da alaka da kwayar cutar Ebola, a yanzu ta kashe mutane 59 a kasar Guinea Conakry. Hukumar kiwon lafiya ta duniya ta bada rahoton cewa mutane 86 suka kamu da cutar da ake kyautata zaton cewa ta Ebola ce a kasar Guinea, kuma daga cikinsu an tabbatar da cewa 13 lallai Ebola ce. Wannan annoba tana yaduwa ne a wasu yankunan karkara na kudu maso gabashin Guinea, ciki harda yankunan Gueckedou da macenta.
Ebola tana daya daga cikin cututtuka masu saurin yaduwa da kwayar halittar cuta ta Virus ke haddasawa, kuma alamunta sun hada da zazzabi mai zafi, haraswa, gudawa da kuma tsiyayar jini. Jami’an kiwon lafiya sun ce ya kamata masu kula da marasa lafiya su takaita cudanya da masu fama da wannan cuta su kuma rika wanke hannayensu a kai a kai.

DUNIYA - MALAYSIA - Malaysia ta ce nazarin da aka yi na bayanai daga taurarin dan adama ya nuna cewa jirgin fasinjarta da ya bace, ya fadi ne a yankin kudancin tekun Indiya. Firayim ministan Malaysia, Najib Razak, ya fada yau litinin cewa nazari sosai da aka yi na hanyar da wannan jirgin sama ya bi bisa bayanan taurarin dan Adam da wani kamfanin Britaniya ya tattara, ya nuna cewa jirgin saman mai lambar tafiya 370 ya fada cikin tsakiyar teku a yamma da garin Perth na Australiya. Yace an sanar da iyalan mutane 239 dake cikin wannan jirgin da ya tashi daga Kuala Lumpur zuwa Beijing abinda ya faru da shi. Wannan sanarwa ta sa tana zuwa a daidai lokacin da wani jirgin ruwan yaki na Australiya yake kokarin kaiwa ga wasu tarkace masu yawa a kan ruwa wadanda wani jirgin sama ya hango a kudancin tekun Indiya, kudu maso yamma da Australiya.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Najeriya, Afirka, Da Duniya Cikin Minti Uku - Litinin - 3'00"