Jami'an kasar Rasha Sun Ce Matashi Ne Ya Kai Hari A Tashar Jirgin Kasar

Masu bincike a Rasha sun gano cewa wani haifaffen Kyrgyz, mai suna Akbarzhon Dzhalilov, ne ya kai harin kunar bakin waken nan na ranar Litini a wani cinkusasshen jirgin kasa a St. Petersburg.

Adadin wadanda su ka mutu a wannan harin ya haura muatane 14, baya ga wasu mutane da dama da ke cikin mawuyacin hali.

'Yan sandan Rasha sun fito da wasu hotunan mutumin da ake zargi wato Dzhalilov, dan shekaru 22 da haihuwa, wanda suka ce an haife shi ne a Osh, sannan ya zama dan Rasha a shekarar 2011.

Masu binciken nakasar Rasha, sun ce Dzhalilov, ya dana bam na biyu a wata tashar jirgin kasa ta St. Petersburg, wanda hukumomi suka gano su ka kuma hana shi tashi. Har yanzu babu kungiyar da ta dau alhakin kai harin, to amma hukumomi na nazarin yiwuwar alakar maharin da kungiyar ISIS.

Shugabannin duniya daga China, zuwa Turai, har da zuwa Brazil, sun bayyana alhininsu game da wannan bala'in. Shugaba Donald Trump, na Amurka, ya kira Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya tabbatar masa da cikakken goyon baya.