Jam’iyyar Republican ta Samu Rinjaye a Majalisun Amurka

Majalisar Amurka

Jam’iyyar Republican ta sake kawace kujerun majalisar tarayyar Amurka ta kuma kara samun yawan kujeru a majalisar wakilai, wanda hakan ya basu rinjaye a majalisun biyu, a cikin shekaru biyun da suka rage ma shugaba Obama.
Kafin nan dai jam’iyyar Democrats ce ke da kujeru 55 daga cikin jimlar kujeru 100 da ke Majalisar, to amma a yanzu jamiyyar Republican ta sami bakwai daga cikinsu, inda ta yi nasara a jihohin Arkansas, da Colorado da Iowa, da Montana da North Carolina da South Dakota da kuma West Virginia.
Sai dai har yanzu ba a sami sakamakon zaben majalisu guda 3 ba a safiyar yau dinnan.

Dama kashi 3 kujerun Majalisar ne aka fafafta akansu a jiya Talata, ciki har da kujerar Kentucky, wadda Shugaban 'yan Republican a Majalisar Dattawa Mitch McConnell dan asalin Kentucky ke kai. Yanzu ya ci wa'adi na shida kenan.

Kakakin majalisar John Boehner yace yanzu ‘yan republican da ke da rinjaye a majalisar, zasu yi aiki akan makamashi da ayyukan yi abinda yace ‘yan jam’iyyar democrat sun shiriritar Yayinda suke kan mulki.