Malam Abdullahi Garba Imam, malami ne a kwalejin Aminu Kano kuma yayi mana karin bayani akan can-canta da tasirin bada kyauta tsakanin masoya a wannan lokaci mai dimbin al'barka wato watan ramadana.
Da farko Malamin ya bayyana mana cewa Alla ya halitta zuciyar dan'adam da kaunar duk wani mai dadada mata da kuma kin duk wani mai kuntata mata, dan haka malamin ya bayyana cewa kyauta nada matukar tasiri a rayuwar dan'adam komai kankantar ta kuwa.
Da muka tambaye shi ko ta wacce hanya ya kamata su bayar da kyautar? malamin ya amsa cewa idan kaji ana neman 'yan uwa ko abokai zuwa kai kyauta to lallai wannan kyauta ba karama bace, dann haka a cewar sa idan aka ba juna a lokacin da ake zantawa ba laifi bane.
Kyautatawa masoyi abin alfahari ne domin kuwa babu koyarwar da ta haramta kyautatawa masoyi, daga karshe ya ce jama'a ku lura ko dabba tasan mai kyautata mata dan haka a rufe ido a kyautatawa juna domin samun kyakkyawar makoma.
Saurari cikakken jawabin a nan.