Jawabin Shugaba Obama Ga Matasan Kasashen Asia

Obama YSEALI

Shugaban Amurka Barack Obama ya fadawa wani gungun matasa jiya Laraba da suka fito daga kasashen kudu maso gabashin Asiya cewa "burin cimma biyan bukatun rayuwa kadai ba zai ishe su ba",suna bukatar daura damara sosai wajen yin jan aikin cimma gurorinsu.

Shugaba Obama ya fada a wajen wani taron musayar yawu da matasa da Amurka ta shiryawa shugabannin matasan kudu maso gabashin Asiya cewa a birnin Laos cewa, matasa sune hanyar ci gaba da gina kasa. Ya jadada bukatar ganin kasashe sun inganta matsayin ilimi da kuma tabbacin ganin an ba ‘ya’ya mata dama, ba yara maza kadai ba.

Obama ya kuma yi amfani da ziyarar tasa zuwa garin Luang Prabang mai tsaunukka, wajen chanja akidar kallon duniya ta ido guda, da dan takarar jam’iyar Republican Donald Trump yake yayatawa da matsayinsa na cewa kullum "Amurka ce ta farko a duniya kafin kowa", da gunagunin da yake yi kan kasashen dake Kungiyar kawancen NATO, da alkawarin da yake yi na gina Katanga kan iyakat Mexico da Amurka domin kange bakin haure.

Ko da yake bai ambaci sunan Trump kai tsaye ba, Obama yace, “ sai dai ba kowa ne a Amurka ya yarda da abinda nake fadi ba.”

Da yake amsa tambayoyin mahalarta taron, shugaba Obama yace, yana fatar sabon shugaban kasar Amurka da zai gaje shi, zai ci gaba (ko zata ci gaba) da hulda da kasashen Asiya dake yankin Pafic, ya kuma ce ya hakikanta majalisar dokokin Amurka zata amince da yarjejeniyar cinikayya da aka cimma da kungiyar da ta kunshi kasashe goma sha biyu.