Kadan Daga Duniyar Tamaula

Mai horas da mai tsaron raga na kungiyar kwallon Kafa ta AS Roma Claudio Tafferal ya bayyana cewar mai tsaron ragar kungiyar Alisson mai shekaru 25 da haihuwa na jin dadin zamansa a kungiyar don haka babu inda zai koma, a yanzu duk da kasancewar kungiyar Liverpool ta matsa kaimi wajan ganin ta saye shi a kakar wasan bana.

Kungiyar kwallon Kafa ta Paris Saint-Germain ta bayyana sha'awarta ta ganin ta dauko dan wasan tsakiya na Chelsea N'Golo Kante, dan shekaru 27 da haihuwa wanda wikilansa suka gana da daraktan wasanni na kungiyar.

Inter Milan tana zawarcin dan wasan baya na kungiyar Chelsea, mai suna Davide Zappacosta, dan shekaru 26 a duniya.

Kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal, tana dab da kammala cinikin dan wasan baya na tsakiya mai suna Caglar Soyuncu, mai shekaru 22 da haihuwa daga kungiyar kwallon Kafa ta Freiburg, dake kasar jamus tuni dai wakilin dan wasan ya tabbatar da cewar tattaunawa ta yi nisa kan batun.

Your browser doesn’t support HTML5

Kadan Daga Duniya Tamaula