Kamfanin Pebble ya Tura Agoguna Miliyan Daya

Yayinda Google da kamfanin Apple ke daukar hanakalin jama’a wajen saida agogona masu amfani da kwakwalwar komfuta kwanan nan, kamfanin agogon Pebble shima yana kan saida nasa kayayyakin sannu a hankali, yana kuma kara inganta kayayyakinsa da saida agoguna.

A Wata hira ta musamman da aka yi da shugaban kamfanin Mr. Eric Migicovsky ya bayyana cewa kamfanin ya tura agogoguna miliyan daya ranar 31 ga watan disambar shekarar da ta gabata. Wannan ya linka abinda aka bada rahoto a watan Maris din shekarar da ta shige, ya kuma ambaci cewa ragowar farashen da kuma wasu kwaskwarima da aka yi a shekarar ya sa sun sami karin ciniki.

Agogunan pebbles sun yi fice, amma kamfanin na fuskantar gasa daga wasu kamfanoni yanzu haka, kamar kamfanonin Motorola, Samsung, LG, da sony wanda suma sun fito da wasu sabbin agoguna masu kwakwalwar komfuta.

Don magance kalubalen da kamfanin ke fuskanta, Mr. Migicovsky ya fada ma dandalin Verge, cewa kamfanin zai kirkiro sabbin kayayyaki a cikin wannan shekarar. Amma dai shugaban bai bada cikakken bayani akan abinda zasu kera ba sai dai yayi shaguben cewa za a yi wasu abubuwan da su sa agogonan su zama fitattu.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Pebble ya tura agoguna miliyan daya - 1'02"