Kamfanin Facebook Ya Shigo Wannan Shekarar Da Kafar Dama

Facebook ya fitar da rahotan dake nuna ribar kamfanin na karuwa inda ta nunka har sau uku a wannan karon, yayin da kasuwar babbar kafar sadarwar ke ci gaba da bunkasa a fadin duniya.

A shekarar da ta gabata kamfanin ya samu riba kimanin Dala Biliyan 1.5 sai gashi kuma ribar tayi tashin gwauron zabi har ta ninka sau uku kimanin Dala Biliyan 5.4.

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg, yace lallai mun shiga wannan shekarar da kafar dama.

Mutanen dake amfani da Facebook duk Wata yanzu haka sun kai Biliyan 1.65, wato sun karu da kaso 15 cikin 100 na yawan mutanen dake amfani da wannan kafa a shekarar da ta gabata.

Rahotanni dai na nunin Facebook na gaban duk wasu kafofin sada zumunci da ake amfani da su a duniya, yayin da kafar ke bunkasa da samun kudin shiga ta hanyar yin tallace tallace ga kamfanoni daban daban.