Kamfanin Nike Zai Yi Ma Super Eagle Sabbin Riguna

Shahararren kamfanin dinka kayan sawa na motsa jiki da suka hada da Jesi, takalmi, wando na ‘yan kwallo a duniya "Nike", ya fitar da sabbin rigunan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya.

Gabanin wasan da Super Eagles zata yi na gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a shekarar 2021 tsakaninta da Saliyo.

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya (NFF), Amaju Pinnick ya ba da sanarwar cewa, kamfanin Nike zai gabatar da sababbin rigunan wasan nan da watan Maris, kafin tunkarar gasar cin kofin duniya.

Kamfanin na Nike ya ce ya kayata rigunan da kuma samar da zabi na nau'uka 65 ga masu bukata a bangarori daban daban da suka hada da hannaye, aljihu, da sauransu.