Wani kamfanin jiragen kasa na kasar Japan ya kakkafa kyammarori da dama domin lura da mashaya masu yawon dare wadanda yawancin lokuta, kan fadi akan titin jirgin har su kaiga jin raunuka ko kuma mutuwa a wasu lokutan, a cewar mai magana da yawun kamfanin.
Kamfanin jirin kasar kudancin Japan ya kafa kyammarori guda hamsin ne a tashar jirgin kasar Kyobashi da ke Birnin Osaka domin dakatar da yawan hadarurrukan da mashayan wadanda yawanci ma'aikata ne ke afkawa a tsakar dare.
Mazauna birnin suna gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali da wadatar jiragen kasar da ke kai su kusan kowane layi suke bukata kuma komin dare, wanda hakan ya sa yawancin ma'aikata kan tsaya su yi shagalin su bayan sun tashi daga ayyukan su harma su yi dare kafin su koma gidajen su.
Yawancin wadanda lamarin ke rutsawa da su na zame wa su fadi ne kokuma wani lokaci su sullube su fada kan titin jirgin saboda tsananin buguwa. Dan haka za a rika lura da kyammarorin ne domin gano duk pasinjan da yake a buge da kuma wadanda basu da lafiya domin shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Kyammarorin za su nuna duk mutanen da ke tafiya da kuma banbanta wadanda ke tafiya daidai da kuma wadanda suke a shaye. kanfanin da ya kaddamar da binciken ya nuna cewar yawancin wadanda abin ya shafa, suna cikin yanayin maye kuma ba su san inda hankalin su ya ke ba.