Kannywood Da Masana'antar Fina Finan Morocco An Kulla Arziki

Hafizu Bello Daraktan Fim

A yau muna nan dauke da bakunci wani babban darakta a masana’antar ta Kannywood, Hafizu Bello inda muka kuma tattauna da shi dangane da sabon yarjejeniyar da masana’antar ta kulla da masana’antar fina finai ta kasar Morocco.

Ya ce ziyarar ta hada mu’amalla ne inda zasu dinga kai fina-finansu kasashen biyu ana haskawa ta gidajen talabijin dinsu da kuma gidajen cinema cinema.

Ya kuma ce zasu dinga hadin guiwa wajan shirya fina finai tare inda ya kara da cewa tsakanin Morocco zuwa Nijeriya kimanin mutane miliyan 70 ne ke ji tare da yin amfani da harshen Hausa, wannan ya karfafawa kasashen biyu guiwa yasa suka aminci da yiwuwar kulla alakar.

Hafizu ya ce akalla nan da wata biyu zasu fara gudanar da muradan nasu , inda yake cewa a yanzu a fina-finan da za’a dinga ganin yan Kannywood a lokaci guda da na ‘yan masana’antar fina finai ta kasar ta Morocco.

Your browser doesn’t support HTML5

Kannywood Da Masana'antar Fina Finan Morocco An Kulla Arziki - 2'44"