Kansas City Chiefs Sun Kafa Tarihi A Wasan Super Bowl

Kungiyar wasan Kansas City Chiefs ta lashe kofin babbar gasar kwallon kafa ta zari-ka-ruga ta Amurka, bayan ta doke San Francisco 49ers da ci 31-20, a wasan karshe da aka kara a jiya Lahadi na Super Bowl, wanda aka yi a birnin Miami.

Bayan da kungiyoyin su ka yi kunnen doki a dai-dai lokacin da aka je hutun rabin lokaci, ‘yan wasan 49ners sun karbe ikon wasan inda suka yi zarra da ci 20-10.

'Yan wasan zari ruga

Amma daga baya sai ‘yan wasan Chiefs, su ka yi kukan kura suka karbe ragamar wasan, dan wasanta Patrick Mahomes ya-kai-ga-gaci tare da taimakon dan wasa Travis Kelce.

An dai kammala wasan ba tare da 49ers sun farfado ba, lamarin da ya kai Chiefs ga nasara.