Dan wasan kungiyar Arsenal Alex Iwobi, yayi wasa da kungiyar Super Eagles ta Najeriya a yammacin jiya Talata, duk da cewa yana fama da ciwon ciki sakamakon cin gurbataccen abinci, wanda yana hana shi yin wasa.
Alex mai shekaru 19 da haihuwa ya bayyana a filin horon yan wasa na Super Eagle, wanda hakan ya kawo karshen jita jitar da ake na cewa har yanzu bai yanke hukunci ba kan ko zai koma Ingila.
Yayin da yan kungiyar ke wasa baki dayansu, shima Iwobi na kokarin dawo da kuzarinsa. Ya dai zagaya filin wasa yana kuma yin wasu wasannin motsa jiki da zasu taimaka masa.
Najeriya dai na fatan kuzarin matashin zai dawo ko zai iya sake taka rawar gani da yayi a kungiyarsa ta Arsenal.
Iwobi ne ya zarga kwallonsa farko a wasan Arsenal da Everton, inda Arsenal ta lashe wasan da ci biyu da babu ranar Asabar.
A halin yanzu dai, yan wasan Najeriya na da cikakkun yan wasan da suke bukata ranar Talata, sai dai har yanzu suna tsammanin zuwan Elderson Echiejile.