Kasar china ta soke dokar haifuwar da daya da ta dade ta na aiki da ita, yanzu kasar ta ba ma’aurata damar haifuwar ‘yaya biyu.
A shekarar aluf dari tara da tamanin ne China ta fidda wannan dokar a wani yunkurin rage yawan al’ummar kasar, wacce ta fi yawa a duk fadin duniya. Tsauraran matakan da aka sa a kasar, ciki har da zubda ciki kan tilas, ya janyo cece-ku-ce a kasashen ketare. Cikin ‘yan kwanakin nan an danganta wannan dokar da dalilin raguwar jama’a a fagen kwadago fiye da kima.
“Duk da damar da aka bada ta haifuwar ‘yaya biyu, mutane da yawa musamman matasa a birane ba sa muradin kara haifuwa bayan daya,” a cewar farfesa Jiang Quanbao na jami’ar Xi’an Jiantong.
Tuni dai larduna 19 a China su ka fara amfani da wannan dokar ta haifuwar ‘yaya biyu, wadda ta ba ma’aurata damar sake haifuwa idan haifuwarsu ta fari mace ce, don a kiyaye matsalar samun gibi tsakanin mata da maza.