Yanzu haka daruruwan mutanen garin Baga da ke gudun hijira a wani sansanin ‘yan gudun jijira a garin Gubuwa cikin kasar Chadi, na neman dauki. Wani wanda ya tsaira ya bayyana cewar anyi arangama da sojoji, ‘yan kato da gora da ‘yan kungiyar boko haram a wani mamaya da suka kawo cikin garin baga, wanda a lokacin wannan arangamar anyi takaddama tsakanin sojoji da ‘yan kato da gora a kan wa zasu shiga gaba don yakar ‘yan ta’addan, wanda daga bisani da ‘yan sandan da ‘yan kato da gora sun gudu don neman mafaka a lokacin da fadan yafi karfinsu.
Ta bakin wanda abun ya faru a kan idon shi yabayyana cewar sai da suka wuni suka kwana a cikin ruwa don neman tsira da rayuwar su. Ya bayyana cewar yanzu haka akwai sama da mata da yara dari biyu da suke a wani gari suna neman agajin gaggawa, don suna wannan gari kuma sun kasa fita balle guduwa. Su dai ‘yan wannan kungiyar na ikirarin cewar suna koyar da mutanen nan karatun a dini, wanda suna wulakanta duk wanda baibi irin tsarinsu ba, wanda kuma yabi suna kyautata musu. Kuma yanzu haka su ‘yan kungiyar nan suna nan suna kame yara ‘yan mata masu kananan shekaru suna dauramusu aure da ‘yankungiyar. Ya bayyanar da cewar sun ga gawawwaki da dama a cikin ruwa da aka kashe.
Yayi nuni da cewar gwamnatin Najeriya bata basu wani taimako da yakamata ba, amma daga isar su kasar Chadi, gwamnatin kasar da jami'an UNICEF sun taresu hannu bi-biyu kuma anbasu taimakon da yakamata. Wani abun duba wa annan shine, gwamnatin Najeriya bata yin komai dangane da magance wannan matsalar, wanda idan aka hada da kasar Chadi suna daukan duk matakan da suka kamata don magance wannan matsalar.
Your browser doesn’t support HTML5