Ko Kun San Amfanin Sanin Matsayin Ku Dangane Da Cutar HIV/AIDS Ko CIDA?

Masu binciken kimiyya da harkokin lafiya sun bayyana cewa bayan kasar Afirka ta kudu, Najeriya ce kasa ta biyu da ta fi yawan jama'a masu dauke cutar kanjamau! koda shike idan aka fahimci ana dauke da cutar da wuri akwai maganin dake rage radadi da kuma gaggawar hallaka mai dauke da ita. ta wacce hanya kuke ganin matasa zasu kare kansu da kuma daukar matakan da suka dace wajan gano yanayin da suke ciki domin daukar matakan gaggawa da suka dace?

Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com