Koch na kungiyar kwallon kafar Real Madrild, bashi da sha’awar jagorantar kungiyar Italiya. Amma yace yana iya komawa kungiyar Milan idan bukatar hakan ta zo. Mr. Carlo Ancelotti, yace bashi da muradin shugabanci klob na kasar Italiya, amma ‘yan kasar ta italiya zasu yi farincinkin hakan.
Ita dai kungiyar Italiyar tana tare da jagorancin Mr. Antonio Conte ne wanda kwantirakin ta kare kuma ba’a sabunta ta ba, sabo da suka da yake samu. Amma shi dai Anceloti ya nuna sha’awarshi a baya ta neman jagorantar kungiyar kasarshi. Kuma bai da niyar barin aikin yauda kulun na shugabanci nan kusa.
Ya kara da cewar duk da yawan shekarun shi bashi da tunanin bari domin kuwa yana jin dalin abun da yake yi. Don tsayuwa da ya keyi a cikin fili wani abun sha’awane gareshi.