Magoya bayan kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid sun bayyana rashin jin dadinsu ga wasu wasanin da kungiyar tayi a kakar bana. Amma Cristiano Ronaldo ya baiwa magoya bayan nasu hakuri da cewa su hada kai don ba wa kungiyar ta Real Madrid goyan baya.
Yau kungiyar zata kara da Paris Saint-Germain a gasar zakarun nahiyar Turai zagaye na 16, za'a buga wasan ne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Wasu na ganin cewar wannan shine kadai kofin da rage wa Real Madrid a bana wace take da damar dauka, kasancewar Barcelona a Laliga tayi mata nisa a mataki na daya da maki 17, a wasannin mako 23, ita kuwa Real Madrid tana mataki na hudu ne a teburin.
Shi kuwa dan wasan Paris Saint-Germain. Angel Di Maria yace duk da tarihinsa a Los Blancos ya ce dangantakarsa da kulob din ta kare, kuma zai dauki mataki zuwa ga abokan hamayyarsa a wasan da zasuyi da Real Madrid yau na gasar zakarun Turai zagaye na 16 karawar farko.
Dan wasan ya buga wasa a kungiyar Real Madrid na tsawon shekaru hudu ya kuma lashe kofin La-liga a kungiyar ya kuma samu nasarar daukar kofin zakarun nahiyar Turai tare da tawagar kungiyar ta Real Madrid.
Daga bisani ya koma Manchester United inda a shekara ta 2015 ne dan wasan ya dawo kungiyar Paris Saint-Germain da taka leda.
Your browser doesn’t support HTML5