Arsenal Tayi Sabon Koci Mikel Arteta

Kungiyar Arsenal ta tabbatar da daukar tsohon dan wasan tsakiyarta Mikel Arteta, a matsayin sabon mai horas da 'yan wasanta.

A yau Jumma'a 20, ga watan Disambar 2019, kungiyar ta kulla yarjejiniyar ta tsawon shekaru uku da rabi tare da Mikel Arteta.

Mikel mai shekaru 37 da haihuwa, ya lashe kofin kalu bale FA CUP, na kasar Ingila a lokacin da yake matsayin dan wasa a kungiyar ta Arsenal, tsawon shekaru biyar da ya shafe, zai ja ragamar kulob din bayan da ta sallami mai huras da 'yan wasanta Unai Emery.

Mikel Arteta

Kafin rike wannan mukami nasa Arteta, yayi aiki a karkashin kocin Manchester City Pep Guardiola a matsayin ma taimakinsa.

Sabon kocin ya bayyana jin dadinsa da kama aiki a tsohowar kungiyar sa da ya buga matasa wasa inda yayi alkawarin kawo gyara a kungiyar.

Arsenal dai tana mataki na 10 ne a gasar Firimiyar bana da maki 22.

A ranar Asabar Arsenal za tayi tattaki domin fafatawa da Everton, sai dai Freddie Ljungberg ne zai ja ragamar a matsayin sa na mai rikon kwarya kafin Mikel Arteta ya karbi jagoranci a wasan gaba.