Kungiyar PSV Ta Sallami Kocinta Mark Van Bommel

Kungiyar kwallon kafar PSV ta sallami mai horas da 'yan wasanta Mark Van Bommel, bayan gaza samun nasara a wasannin da ya jagoranta a bana.

Kungiyar ta ce Mark Van Bommel, ya yi nasara a wasannin biyu ne kacal a cikin wasanni takwas da ya jagoranta a bana.

Bommel mai shekaru 42 da haihuwa, wanda kuma tsohon dan wasan Barcelona ne, ya karbi aiki a kungiyar ta PSV a shekarar 2018 bayan da ya maye gurbin Phillip Cocu.

Kungiyar PSV dai a yanzu haka tana mataki na hudu a teburin lig, da banbancin maki goma tsakani ta da Ajax, wacce take saman teburin lig na kasar Holland.

A ranar Lahadi da ta gabata kungiyar Feyenoord ta lallasa ta ci 3-1.