Kungiyar Wasan Matasan Flying Eagles Sun Sauka A Kasar Senegal

Masoya Kwallon Kafa Su Na Dokin Fara Gasar Cin Kofin Duniya

Kungiyar kwallon kafar matasan Najeriya, Flying Eagles sun sauka kasar Senegal domin buga wasan neman samun shiga gasar neman guri na wakiltar nahiyar Afirka na wannan shekarar, a wasan cin kofin matasa na Duniya.

Tawagar ‘yan Najeriyar dai wadda ta hada da matasa su 21 da kuma jami’an kungiyar guda goma, sun isa filin saukar jiragen saman Dankar na kasa da kasa, da missalin karfe uku na asubahin jiya Alhamis, inda aka kwashesu zuwa Alafifa Otel inda zasu zauna na wucin gadi, kafin su tashi su koma wani Otel mai suna Ngor Diarama.

Kungiyar matasan Flying Eagles, zasu fara gasar ne da neman nasara a kare kambunsu karo na bakwai a tarihi, inda zasu fara karawa da kasar Senegal ranar Lahadin nan mai zuwa, zakuma su fuskanci kasar Congo a ranar Talata mai zuwa. Wasan rukunun su na karshe zai zamanto ne da kasar Ivory Coast ranar sha hudu ga watan Mayu.

Duk kasashen dasuka samu nasarar kaiwa ga wasannin kusa da karshe to zasu wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin matasa na duniya, da za’ayi a kasar New Zealand.