Kungiyoyin Mata A Jihar Borno Sun Yi Rokon Da A Sako Dalibai Mata Da Aka Sace - 23/4/2014

Kungiyoyi dabam-dabam na mata a Jihar Borno sun roki duk wani wanda zai iya taimakawa a sako dalibai yara mata da aka sace daga makarantar sakandare ta Chibok da ya taimaka domin ganin an yi hakan cikin gaggawa.

Wadannan mata, wadanda wasunsu suka rika barkewa da kuka a saboda jimamin abinda ya faru, sun ayyana cewa wadannan yara ne da ba su san fari ba balle baki, wadanda ba su da alhakin komai na abubuwan dake faruwa, don haka bai kamata a ce an sace su ba.

Ga cikakken bayani nan daga wakilinmu Haruna Dauda, inda za a fara da jin Farfesa Hauwa Abdu Biu...

Your browser doesn’t support HTML5

Mata A Jihar Borno Sun Yi Tur Da Sace dalibai Mata - 3'14"