Kwallon Kafa: Yadda 'Yar Najeriya Ta Yi Zarra a Belarus

Emuidzhi

An karrama yar Najeriyar Emuidzhi Oghiabekhva a taron ba da lambar yabo da aka gudanar a kasar Belarus.

Oghiabekhva ta zira kwallaye 44 a cikin wasannin 26 da aka buga a gidan abokan wasansu.

'Yar wasan mai shekara 29, ta zama ta 4 cikin hazikan 'yan wasan 2019 na Najeriya.

Ta taba zira kwallaye 3 cikin wasa daya, har yanzu ta zira kwallaye bakwai cikin karawa biyar, duk a cikin kakar wasan 2019 wanda aka kammala.

Ganin hazakarta, ya sa aka tsawaita mata kwantiraginta zuwa Satumbar 2020, za kuma ta ci gaba da zama a kasar har lokacin karewar kwantiragin.