WASHINGTON, DC —
Yayin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da binciken tashin bam jiya a Nyanya, dab da inda aka smau tashin bam na kwanakin baya, yawan mutanen da bam din ya kashe ya karu kamar yadda kakakin ‘yan sandan Abuja, Altine Daniel ta yi mana bayani
Haka kuma, kakakin ‘yan sanda ta ce ba zata yi karin haske kan ko su wanene ake zaton sun kai harin ba tun da ana bincike, amma kuma ta ce an samu wasu bama-baman har guda uku, wadanda Allah Ya sa ba su tashi ba.
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kira wani taron gaggawa na manyan jami’an tsaron kasar domin tattauna wannan al’amarin.
A halin da ake ciki, su ma shugabannin addini da malamai su na ci gaba da yin tur da wannan harin bam. Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, shi ne shugaban majalisar malamai ta babban birnin tarayya Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5