Wata kungiya me zaman kanta da kuma ke kara wayar da kan ‘yan kasa dangane da fahimtar dokokin kasa, wato kungiyar wayarwa, ilmatar da jama’a daga tushe, wadda take a turance, Civic "Education for Grassroots Mobilizations, Shugaban wannan kungiyar, Malam. Balarabe Rufa’I, yayi nuni da cewar duk inda kaga ansamu tashin hankali to ba komai ke kawo hakanba illa rashin adalci, kuma a wannan karon kungiyoyi sun taka mahiman rawa wajen wayar da kan al’uma, don bin dokoki da tsare-tsare.
A wannan mataki da ake kai ganin an kamala zabbubuka to lallai yakama ta jama’a suba ma gwamnatoci hadin kai don su samu su gudanar da ayyukan su na cigaban kasa yadda yakamata, yaka mata a manta da banbance banbance na siyasa, a meda hankali wajen gani an bama gwamnatoci hadin kai don kyautata rayuwar al’umah da inganta tsaro, tattalin arzikin kasa da dai duk abubuwa da suka kamata.
Wani abun kara jawo hankalin al’uma anan shine jama’a musamman matasa su meda hankali wajen amfani da kafofin sadarwa na yanar gizo don cinma manufa mai amfani da cigaban al’uma. A zahirin gaskiya, wannan wani lokaci ne da yakamata matasa suyi amfani da wannan dammar don wayarwa, ilmantarwa, da fadakarwa da duk wasu abubuwa da kan cutar da jama’a ta amfani da hanyoyin sadarwar intanet.
Mutane su sani cewar idan sukayi amfani da wannan yanar gizon ta yadda yakamata to lallai ba shakka kasa zata cigaba kuma za’a samu Karin yawaituwan ilimi a cikin jama’a, da kuma magance matsaloli kamar su rashin tsaro, rashin tarbiyya, da dai duk wasu abubuwa da zasu kawo rashin cigaban kasa baki daya. Don haka ana kara kira ga matasa su taimaka su bama wannan sabuwar gwamnatoci duk wani hadin kai da yakamata don gina kasar baki daya.