Lokacin Lalaci Ya Wuce In Ji Fatima Sa'idu

Kayayyakin Yara Kanana

Lokaci yayi da mata zasu tashi tsaye wajan domin neman na kansu domin lokaci lalaci ya wuce.

Malama Fatima Sa’idu, wata uwa mai ‘ya’ya uku kuma ‘yar kasuwa tayi wannan furushi ne a wata tattaunawa da wakiliyar Dandalinvoa, a birnin Kana, Baraka Bashir.

Tace ta fara sana’ar sayar da kayan yara bayan da ta kamala karatun ta, boko ta kara da cewa dalin aure yasa ta canza gari kuma neman aiki ya ci tura inji Fatima Sa’idu wacce aka fi sani da Maman Nabila

Ta ce a da tana garin Kaduna da zama bayan kamala karatun ta na boko ta nemi aiki bata samu ba a garin Kano, kawai sai ta maida hankali ga sana’ar sayar da kayan yara, inda take kawata ‘yayata da irin kayayyakin da take sayarwa.

Tana mai cewa a mafi yawan lokuta idan ta fita da ‘yaya walau asibiti ko unguwa sai jama’a ke tambayar a ina ta sayo wa ‘yayanta kayayyaki da suke sanye dasu, daga nan ne ta fara tara kwastamomi inji maman Nabila, kamar yadda wasu ker kiranta. Na fara sana’ar sayar da kayan yara bayan na kamala karatun na, na book bayan da uare ya canza min gari kuma neman aiki ya ci tura inji Fatima Sa’idu wacce aka fi sani da Maman Nabila

Ta ce a da tana garin Kaduna da zama bayan kamala karatun ta na boko ta nemi aiki bata samu ba a garin Kano, kawai sai ta maida hankali ga sana’ar sayar da kayan yara, inda take kawata ‘yayata da kaya masu kyau

A mafi yawan lokuta idan ta fita da ‘yaya walau asibiti ko unguwa sai jama’a ke tambayar a ina ta sayo wa ‘yayanta masu kyau, daga nan ne ta fara tara kwastamomi inji maman Nabila, kamar yadda aka santa dashi.

Ta kara da cewa ko yanzu ta sami aikin gwamnati lallai zata karba hanu, biyu sannan ta kuma cigaba da sana’ar data ke yi na sayar da kayan yara.

Your browser doesn’t support HTML5

Lokacin Lalaci Ya Wuce In Ji Fatima Sa'idu - 3'03"