London: Wata Fasahar Zamani Za Ta Fara Tsamo Masu Laifi A Bainar Jama'a

'Yan sanda a birnin Landon za su fara amfani da na’urar kyamara mai tantance fuskoki don zakulo mutanen da ake kyautata zato sun aikata wani laifi daga taron jama'a, wannan wani ci gaban fasahar zamani ne mai cike da takaddama wanda ya janyo damuwa akan tabarbarewar hakkokin sirrin bil’adama.

A ranar Jumma'a ne rundunar 'yan sandan birnin ta sanar da cewa, bayan an yi wasu gwaje-gwaje, kyamarorin za su fara aiki a cikin wata guda a wasu wuraren da ake kyautata zaton ana aikata manyan laifuka sosai kuma za su yi aiki tsawon sa’o’i 5 zuwa 6.

Bisa ga bayanan sirri za a zabi wuraren da za a kafa kyamarorin amma 'yan sandan ba su bayyana su ba, ko yawan wuraren, ko kuma adadin kyamarorin da za a kafa.

Wannan matakin da hukumomin birnin su ka dauka na amfani da wannan fasahar ya sabawa gargadin da kungiyoyin kare hakkokin bil’adama, da kwararru da kuma kungiyar Amnesty International su ka yi a cewar Anna Bacciarelli, mai bincike a kungiyar Amnesty.

"Fasahar gano fuskar masu laifi wata babbar barazana ce ga hakkokin bil’adama, ciki har da hakkokin sirrin mutum, da ‘yancin bayyana ra’ayi, da gudanar da taro cikin lumana da kuma kawar da bambanci a cewar Bacciarelli.

'Yan sandan London sun ce na’urar mai gano fuskoki, wadda ke aiki daga wani kamfanin fasahar Japan da ake kira NEC, na nazarin fuskoki a taron jama’a don gano ko fuskokin wadanda ake nema “ruwa a jallo” ne, wato kusan mutane 2,500 da suka aikata manyan laifuffuka a birnin, ciki har da laifukan da suka shafi amfani da wuka ko bindiga, ko keta hadin yara kanana.

"A matsayin mu na 'yan sandan zamani, na yi imanin cewa muna da damar muyi amfani da sabuwar fasaha don kare jama’a a birnin Landon," a cewar Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan birnin Nick Ephgrave a cikin wata sanarwa.