Lucas Perez: Dalilina Na Kin Komawa Barcelona

Dan wasa Lucas Perez, mai shekaru 31 da haihuwa, ya bayyana cewa bai shirya barin kungiyar sa ba, ba ya bukatar sake cusa ma kansa bakin ciki a kan duk wani mataki da zai dauka yanzu.

Lucas ya jaddada cewa bai taba tunanin komawa Barcelona ba daga kungiyarsa ta Alaves, wanda hakan na iya sa shi cikin wani yanayi na kakani-kayi, ko kuma ya koma dan kallo, kamar shekaru biyu da ya yi tare da Arsenal a gasar Firimiya Lig.

A tsakiyar kakar wasanni ta bana ‘yan wasan Barcelona da dama sun tafi hutun jinya, wanda hakan yasa suka rasa irin su 'yan wasa Luis Suarez da Ousmane Dembele, wadanda suka ji rauni sosai, kana hakan yasa aka basu dammar dakko wasu sabbin 'yan wasa na masu zura kwallo.

Ousmane Dembele

Ko kamun nan, Perez wanda ya taka leda sau 21 a kakar wasannin biyu da ya yi Gunners, an dai ta alakanta shi da barin kungiyar don komawa Catalans a watan Janairu, yayin hada-hadar ‘yan wasa.