Mai Gadi Ya Hallaka Wani Dalibi Saboda Gyadar Kashu

Jami’an ‘yan sanda a jihar Enugu sun damke wani mai gadi da ake zargi da hallaka wani dalibi matashi mai suna Ugochukwu Oduburu, da ya tsainki dan itacen Kashu.

Mujallar Daily post ta wallafa cewa rahotannin sun ce matashin mai shekaru goma sha bakwai da haihuwa dake karatu a GTC Akama, dake karkashin hukumar Ezeagu, ya yi ta zuwa dibar kashu ne kafin ya hadu da wani mai gadin kamfanin sarrafa gyadar kashu, wanda akai zargin ya harbe shi har lahira.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a jawabin da ya aikawa manema labarai a jihar, ya bayyana cewa lamafin ya faru ne a ranar 17 ga watan Fabarairu, na wannan shekarar da muke ciki.

Matashin wanda ma’aikacin wucin gadi ne na tsikar ‘ya’yan iatcen kashu, na zama ne tare da dan’uwan shi a unguwar da ya je tsinkar ‘ya’yan kashu din, inda aka harbe shi har lahira.

Wanda ake zargi da aikata kisan ya yi amfani ne da bindigar tokay a harbe matashin har lahira.

Jami’in ya bayyana cewa ana sa ran tasa keyar wanada ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.