Mai Horar da ‘Yan Wasan New Castle ya Daukaka Kara Zuwa Hukumar Kwallon Kafar Ingila

Mai horar da ‘yan wasan New Castle ya daukaka kara zuwa Hukumar kwallon kafar Ingila ta FA, bayan da aka baiwa dan wasansa Fabricio Colocini katin sallama, yayin da kungiyar Sunderland ta doke ta a karawar cikin gida.

An baiwa kyaftin din kungiyar ta New Castle jan katin ne kafin a je hutun rabin lokaci, inda daga karshe aka kuma lallasa su ci 3-0.

An sallami shi ne bayan da ya yi karo da dan wasa Sunderland Steven Fletcher a yankin buga penerti, lamarin da ya sa aka ba da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Wannan kora da penartin da aka baiwa Sunderland, sun janyo cecekuce yayin da Sunderland ta samu nasarar lallasa New Castle a karo na shida a jere, wato kuma haduwar da suke yi.

Adam Johnson da Billy Jones da kuma Fletcher ne suka zirawa Sunderland kwallayenta.

News Castle din ta bayyana daukaka karar ta ta ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta kwatanta korar da akawa dan wasanta a matsayin kuskure a ranar Lahadi.

A gobe Talata ake sa ran wani kwamitin dake kula da daidaita al’amura zai saurari wannan kara da New Castle ta shigar.

Idan dai har ba a sauya wannan matsyar da alkalin wasan ya dauka a wasan ba, hakan na nufin ba zai buga wasan da kungiyar za ta yi da Stoke City a ranar Asabar mai zuwa.