Makaranta Ko Sana'ar Bola

Yaron Bola

A dai dai lokacin da ake yaki da safarar jama’a da kuma bautar da kananan yara ta hanyar saka su ayyukan kwadago,yanzu haka wata matsalar itace ta neman kayan bola da wasu kananan yara ke yi ba tare da la’akari da illar dake akwai ba.

Wadannan yara da basu wuce shekarun zuwa makaranta ba,amma sukan wuni a inda ake zubarda shara ko kuma dagwalar bola,duk kuwa da hatsarin dake akwai.

Alal misali,Ibrahim Sani wani almajiri ne da aka kawo karatun allo,kuma shekarunsa basu wuce 13 ba, yace rashin kudi ke tilasta su neman gorunan roba,akan bola da masu sana’ar zobo ko kunun zaki ke saya a hannunsu domin amfani dasu.

Kamar Ibrahim Sani shima Yahya Abubakar wanda dalibin makarantar firamare ne dake aji biyar, yace shima neman kudin yake yi akan bola ba tare da tsoro ba.

To wai ko yaya iyayen gidan wadannan yara ke ji? Mallam Babayo na cikin masu sayan kayan bolan da wadannan kananan yara ke nemowa,yace su a wajensu babu matsala.

Koma da menene dai masana na danganta wannan matsala da rashin kulawan iyaye,yayin da wasu kuma ke danganta shi da talauci dan manin da ba’a rabuwa da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Makaranta Ko Sana'ar Bola - 2'26"