Duk da cewar an rufe hada hadar zaratan ‘yan wasan kwallon kafa ta duniya har sai zuwa watan Janairu 2018 kafin a bude. hakan bai hana kungiyoyin kwallon kafa su kulla yarjejeniyar ciniki tsakaninsu ba sai dai koda an cimma matsaya akan sayen dan wasa dole sai an bude kasuwar hada hadar a watan Janairun dubu biyu da sha takwas kamar yadda doka ta tanadar.kafin dan wasan ya fara taka leda a duk kungiyar da ya Koma.
A yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta kammala sayen tsohon dan wasanta Diego Costa daga kungiyar Chelsea akan kudi sama da fam miliyan £60.
Ita kuwa Manchester United na kasar Ingila na harin sayen dan wasan gaba na Atletico Madrid mai suna Antoine Greizmann, mai shekaru 26, da haihuwa akan kudi fam miliyan £88.
Dan wasan tsakiya Eden Hazard, na Chelsea, na shirin sabunta kwangilansa a kungiyar na tsawon wani lokaci.
Kungiyoyin Manchester United, da takwararta Real Madrid, ta kasar Spain, sun shiga sahu daya wajan takarar zawarcin dan wasan gaba daga Juventus, mai suna Paulo Dybala, mai shekaru 23, da haihuwa,
Real Madrid, tana shirye shiryen ganin ta sayo dan wasan tsakiya na PSG, mai suna Jillian Draxler, mai shekaru 23, a duniya, da zaran an bude cinikayyan ‘yan wasa a watan janairun 2018.
Your browser doesn’t support HTML5