Manchester City Zata Barje Gumi Da Hull City

A cigaba da wasannin la-liga na shekara 2016/2017 mako na talatin da daya yau kungiyar kwallon kafa ta Villarreal zata karbi bakuncin Athletic Bilbao da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar, kamaru da Chadi.

Gobe idan Allah ya kaimu Espanyol zata kara da Alaves, Real Madrid kuma ta fafata da Atletico Madrid, Sevilla da Deportivo, Malaga zata barje gumi da Barcelona.

A kasar Ingila kuwa gobe Asabar 8/4/2017, za'a fafata a bangaren Firimiya lig na shekarar 2016/2017 mako na 32, Tottenham zata gwabza da Watford, Stoke city da Liverpool, Westham United da Swansea sai Manchester City da Hull city, Westbromwich da Southampton, Middlesbrough da Burnley AFC Bournemouth zata kara da Chelsea.

Za'a fara wasan ne da misalin karfe sha biyu na rana agogon Najeriya har zuwa karfe biyar da rabi na yamma.

Your browser doesn’t support HTML5

Manchester City Zata Barje Gumi Da Hull City - 2'41"