Masu Gudun Hijira Sun Samu Muhalli

Majalisar dinkin duniya, ta gina wasu rukunin gidajen na dindindin wanda zai kasance matsuguni ga ‘yan gudun hijira, a Daudu, dake karamar hukumar Guma a jihar Benue.

Wadannan rugunin gidaje sune na farko da majalisar dinkin duniya ta samar da zai kasance matsuguni na dindindin, ga wadanda wani bala’I ko wani tashin hankalin ya shafa har sai sun samu natsuwan dazasu koma yankunansu na asali.

Da take kaddamar da rukunin gidajen wakiliyar kula da ‘yar gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a Najeriya, da kasashen Afirka ta Yamma Madam Angel Atangana, tace kasancewar jihar Benue, ta sha fama da rikicen cikin gida da matsaloli tsakanin makiyaya da manoma ya saya fiye da mutane dubu dari ukku gujewa dag mahallansu.

Ta kara da cewa babban abinda ‘yan gudun hijiran ke bukata shine tsaro da samun muhalli, masamman ga mata da yara.

Tana mai cewa da damarsu suna bukatar abinci da sanao’i, da zasu inganta rayuwarsu shi yasa hukumar zaben wadansu da ta kai jamhuriyar Benin, domin yin nazarin wani shirin Noma, da kiwon dabbobi da kifi na zamani domin samarwa ‘yan gudun hijirar.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Gudun Hijira Sun Samu Muhalli - 3'30"