Don iya dogaro da kai, dama tallafawa iyali da ma yan’uwa. Wata baiwar Allah, da take sana’ar Haja sama da shekaru Ashirin, tayi muna karin haske dangane da yadda take gudanar da sana’ar ta.
Ita dai Malama. Jamila Ibrahim, tace ta fara wannan sana’ar tun tana yar karamar yarinya, wanda ta kasance tana tai maka ma magaba tanta a duk lokacin da suke wata hidima ta kasuwanci, wannan shiya bata sha’awar itama tayi wannan sana’ar.
Wanda tace lokacin da take makarantar kwana, idan ta dawo hutu sai tayi wasu abubuwa da zata dinga siyarwa kamin ta koma makaranta. A wannan har tasamu taje jami’a kuma ta gama, yanzu kuma tana sayar da atamfofi, shaddoji, yadduduka, da dai kayan mata kowane iri. Ta kuma kasance tana da ‘yaya kuma sana’ar ta bata hanata yin komai ba, takan kuma taimakama mijinta da ‘yayanta harma da yan’uwanta akowane lokaci bukatar hakan ta taso.
Ta kuma yi kira da ‘yan’uwanta mata da su tashi tsaye wajen neman na kai don dogaro da kai.
Your browser doesn’t support HTML5