Mata Masu Dauke Da Juna Biyu Sun Samu Tallafin Kudi

Pregnant women watch television as they wait in the prenatal ward at a maternity hospital in Sierra Leone.

Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya,UNICEF, da hadin guiwar uwar gidan gwamnan jihar Adamawa Hajiya Maryam Bindo, sun kaddamar da shirin bada tukwuicin kudi ga matan dake zuwa awon ciki a jihar ta Adamawa.

Wannan wani yunkuri ne na magance matsalar mace macen mata yayin haihuwa, bincike ma na nuni da cewa kimanin mata dari biyar ne daga cikin mata dubu dari ke mutuwa a lokacin haihuwa a kudanshin Najeriya, yayinda dubu daya da dari biyu ke mutuwa daga cikin dubu goma lokaci haihuwa a arewacin Najeriya, baya ga karuwan adadin matan dake fama da matsalar yoyon fitsari da dalilin matsalar haihuwa.

Domin magance wannan matsalar yasa UNICEF, tare da hadin guiwar uwargidan Gwamnan jihar Adamawa, Hajiya Maryam Bindo, daukar nauyin wannan sabon shirin lafiya da nufin rage mace macen mata masu dauke da juna biyu da kuma kananan yara a jihar Adamawa.

Da take kaddamar da wannan sabon shiri a karamar hukumar Fufure Hajiya Maryam Bindo, tace bullo da wannan shiri ya zama wajibi domin magance matsalar mace macen mata yayin haihuwa.

Saurara domin karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Mata Masu Dauke Da Juna Biyu Sun Samu Tallafi - 3'13"