Ana tuhumar mukaddashin shugaban makarantar sakandaren Gwamnati dake Tunga-Minna a jihar Niger mai suna Mallam Kuyizhi da yin lalata da wata yarin ‘yar makaranta mai shekaru goma sha shida da haifuwa wanda yayi sanadiyar yarinyar ta samu juna biyu.
Biyo bayan wannan tuhuma da ake masa, an kai Kuyizhi gaban cibiyar kare hakkin kananan yara ta kasa a kan laifin zargin cewa ya yiwa wata yarinya mai shekaru 16 juna biyu.
Da take shugabantar wani zama akan batun jiya Laraba a Minna, babban darektan cibiyar, Hajia Mariam Kolo, ta fada cewar wata malama ce ta kawowa cibiyar wannan kara bayan da marikiyar daliban ta shaidawa makarantar cewar wani malami ya yimata ciki.
Kolo tace za a mika wannan kara ga ‘yan Sandan ciki masu binciken laifuka don su ci gaba da binciken wannan batu.
Ta bada tabbacin cewar yarinyar zata samu adalcin hukuma, Hajia Kolo tace an riga an kai yarinyar asibiti agwada lafyarta, sai dai zamu tabbatar da gani an yi mata adalci.
Babban darektan cibiyar ta kare hakkin yara tace yarinyar ta fada mata cewa, Malam Kuyizhi ya kwanta da ita sau uku a ofishinsa sai ya bata Naira hamsin da kuma Naira dari ta dau mota.
Yarinyar mai juna biyun ta tuhumi malamin da bata wasu kwayoyin magani bayan ta bashi labarin tana da juna biyu sai dai taki shan kwayoyin da ya bata.
An rawaito kalaman Hajia Mariam Kolo tana cewar, Mallam Kuyizhi ya tabbatar da ya kwanta da yarinyar ‘[yar shekara 16, sai dai yace itace ta masa karuwanci har ya amince ya aikata wannan abu.
Mallam Kuyizhi ya shaidawa ma’aikatarta cewa ya shigeta amma bai sake ruwan jikinsa a cikin farajinta ba, don haka ba shine ya mata ciki ba.