Matasan Nijeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu kan dage zaben Nijeriya da aka yi. Wani matashi mai suna Aminu Ibrahim ya ce shi sam bai ji dadin dage zaben ba, to amma ya na fatan Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi ga Nijeriya. To amma ya ce idan ba a iya warware matsalolin tsaro cikin shekara da shekarun da aka yi ba, babu yadda za a yi a magance cikin dan lokaci kankani.
Ita ko wata mai suna Fatima ta ce daga zaben ya takura masu musamman saboda an ce ba za a ba su hutun makaranta ba. Ita kuwa mai suna Ramla cewa ta yi ita ma ba ta ji dadin dage zaben ba saboda ga dukkan alamu wata makarkashiya ce don haka kamata ya yi a gudanar da zaben don hankali ya kwanta. Shi ma wani da bai bayyana sunansa ba, ya ce daga zaben bai masa dadi ba.
Shi ma ya ce abin da aka kasa yi cikin shekaru hudu da su ka gabata, babu yadda za a iya yi cikin wata daya da wani abu. Ya ce jiya ya kai kusan karfe 12 na dare bai yi barci ba saboda tunanin makomar al’amarin. Ya ce duk wanda ya ga Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya Furfesa Attahiru Jega zai san cewa ba da son ransa ya dage zaben ba. Y ace ga dukkan alamu jam’iyyar da ke mulki c eke son dage zaben saboda wani dalili na son rai.
Your browser doesn’t support HTML5