An yaye wasu matasa wajen 2000 da su ka koyi sana’oin hannu daban-daban. Gwamnati ta ce ta kashe sama da Naira Miliyan 680 wajen horar da matasan da kuma samar masu kayan aiki don taimaka masu har su iya zama da gindinsu. Wannan kuwa wani bangare ne na shirin nan da ake kira SURE-P da gwamnatin Najeriya ta bullo da shi amfani da rarar kudin man fetur wajen tallafa ma mutane su mike.
Alhaji Hassan Nuhu, babban Daraktan kula da wannan shirin a jihar Naija, ya bayyana wa wakilnmu a jihar ta Naija cewa manufarsu ita ce su “tabbatar da cewa matasa sun sami ayyukan yi a mataki na farko; da kuma yaki da talauci a mataki na biyu; na uku kuma kara samun tsaro da natsuwa a kasa domin idan matashi majiyin karfi bai da aikin yi, bai da sana’ar yi sannan kuma gas hi da karfi sosai, to ka ko san ba za a zauna lafiya ba a kasa.”
Ita kuwa Malama Amira Aliyu, daya daga cikin wadanda su ka koyar ma matasan, ta ce su na bin matasan ne har zuwa yankunan karkara don koyar da su. Don haka ta ce su kan fuskanci kalubaloli iri-iri. Ta ba da misali da yadda su ka je wani garin da ma ba su jin ko Hausa, kuma basu da saurin fahimtar bayani.
Ita ma wata mai wani shiri kwatankwacin na Sure-P mai suna A’sha Babangida, wadda ita ma ta halarci bukin yaye matasan, ta yi kira ga matasan da su ka amfana da wannan shirin na Sure-P, da su canza rayuwarsu ta zama ta alheri ta yadda za ta amfani su kansu da ma al’umma baki daya.
Wasu daga cikin matasan da su ka amfana da shirin sun yaba da tallafa masu da aka yi, tare da alkawarin su ma za su taimaki na kusa da su da ma al’umma baki daya da amfanin da su ka samu daga wannan shirin.
Your browser doesn’t support HTML5