WASHINGTON DC —
Dandalin VOA ya leka taron matasan da muryar Amurka ta shirya a Kaduna a makon da ya gabata, wakiliyar muryay Amurka Baraka Bashir tayi hira da shugaban matasan jam'iyar APC na jahar Kaduna Umar Yahaya inda yake cewa.
"Rashin adalci na daya daga cikin makasudin dake haifar da tashin hankali kuma abinda suke gudu shine rikici" matasan dai sun nuna fahimtarsu da kuma bada shawarwari musamman ta yadda hukumomi zasu zasuyi ma jama'ar su adalci domin samun cigaban al'uma.