Matasa Sun Kashe Wata Yarinya Mai Tabin Hankali a Bauchi

Hoton Yarinyar da aka kona a Jahar Bauchi

Bisa ga irin takaicin kisan wata yarinya mai tabin hankali da matasa suka yi akan kuskure, wacce suka yi tunanin ‘yar kungiyar boko haram ce. Shugabannin matasa sun yi kira ga matasa gaba daya sakamakon wannan aika-aikar da ta faru.

Aminu Sule na kungiyar (Network for Justice) cewa yayi, “ya kamata masu taimakawa gwamnati ko jami’an tsaro game da fada da boko haram suyi taka tsan-tsan kuma su daina daukar doka a hannunsu, su tabbatar sun hada hannu da jami’an tsaro kafin su aiwatar da duk wani abu makamancin haka”.

Daga karshe ya kara da cewa matasa sune ginshikin kowace al’umma kuma su ya kamata su zama masu natsuwa da kiyaye dokokin kowace al’umar da suke cikinta. Domin kuwa idan matasa suna daukar doka a hannusu akwai yiyuwar su dinga yin abinda za su yi nadamar aikatawa.

Your browser doesn’t support HTML5

kisan wata yariya a bauchi

##caption:Matasa sun kona wata yarinya bisa kuskure a garin Bauchi.##