Matasa Sun Sha Alwashin Hana Amfani Da Kalmar Batsa Wajan Tallar Magani

Dangane da matsalar yin anfani da kalmomin batsa da yawancin masu tallar maganin gargajiya keyi, matasa sun kuduri aniyar tabbatar da kawar da wannan a cikin al'umma gaba daya domin lallai hakan bai dace da kowace irin al'umma ba.

A wata hira da wakilin muryar Amurka Ibrahim Ka'almasih Garba yayi da shugaban kungiyar hadin kan matasa Isyak Abdul, ya bayyana cewa sunyi meeting har sau biyu kuma sun dauri aniyar gabatar da duk wanda suka kama na irin wannan tallar a bainar jama'a a gaban hukumar hukuma.

Wannan matsalace babbba domin duk inda kananan yara suke kuma ana yin amfani da irin wadannan kalmomin to tamkar ana koya masu wata muguwar tabi'a ce.

Daga karshe yayi kira ga dukkan masu irin yin hakan da su daina, da kuma bada tabbacin daukan matakai akan sabawa dokar.

Your browser doesn’t support HTML5

matasa da tallar batsa

##caption:Matasa na adawa da tallar batsa.##