Matasa Wacce Irin Kyauta Kuka Ba Masoyan Ku Domin Azumi

Shirin samartaka na wannan makon ya ji ra’ayoyin matasa ne akan wannan lokaci na azumin Ramadana musamman kamar yadda masu iya Magana suka ce idan rawa ta canza, kida ma canzawa yake! Ta dalilin haka ne muka yi masu tambaya kamar haka, wane tanaji kayi wa masoyiyarka domin ramadana?

Matashin farko ya bayyana mana cewar gaskiya shidai kam babu wani abin da yayi domin kuwa a cewar sa, yana kan shirin aure ne a yanzu haka, kuma bayan azumi yake sa ran za’a daura masa aure dan haka a takaice yana cikin wani yanayi na jin jiki, daga karshe ya kara da cewa ita ke taimaka masa da wasu abubuwan makamantan kayan buda baki.

Yawancin matasan sun bayyana ra’ayoyin su mabanbanta amma yawanci sun nuna cewar sun yi kamar yadda al’ada ta tanada masu wato sayen kayan buda baki iya gwargwadon halin da suka ga zasu iya domin wannan lokaci na ibada.

Da muka nemi jin tabakin su akan ko suna ganawa kamar yadda suka saba, yawanci sun nuna cewa sai dai kira ta waya, domin a cewar su, yawaita ibada ne mafi akasarin ayyukan da suka sa a gaba. Amma fa duk da haka akwai wadanda suka nuna cewa sukan gaiyaci abokan huldar su domin zuwa hira kuma har ma su bada baki a gidan masoyan su.

Ga cikakkiyar hirar.