Matasa Zasu Taka Rawarsu a Siyasar Jamhuriyar Nijar

Hama Amadou

Jamiyar Lumana Afirka, ta jamhuriyar Nijar, ta zabi Malam Hamma Amadou, a matsayin shugabanta, duk da kasancewarsa, baya kasar.

Mahalarta taron,sun tantance matsayi da akidar uwar Jamiyar, ta Lumana Afirka, tare da sauya kwamitin ta na zartarwa, da samarda wani sabon kwamiti, mai kunshe da matasa.

Garo na biyu kennan jamiyar ta Lumana Afirka, gudanar da taron ta amma wani abun mamaki shine, ana wannan taron ne batare da shugaban Jamiyar, Malam. Hamma Amadou, wanda ke gudun hijira a kasar Turai.

Bayan zaben sabin shuwagabani, jamiyar ta Lumana Afirka, taron na kasa ya tabbatar da Korar wasu kusochin jamiyar, da suka bujirewa uwar jamiyar, inda suka nuna goyon bayan su ga Gwamnatin shugaba Muhammadu Issufu.

Zabe a Nijar - 3'09"