Menene Ra'ayin Ku A Kan Matakin Korar Malamai Sama Da Dubu 21, A Jihar Kaduna?

Biyo bayan korar malaman makarantar firamare sama da dubu 21, da gwamnan jihar Kaduna yayi, jama'a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akan lamarin, me nene ra'ayin ku akan wannan mataki da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka?

Muna bukatar sakonnin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com