Dan wasan tsakiya na Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma dan kasar Jamus, Mesut Ozil, ya kafa tarihi a bangaren jefa kwallo a raga, inda ya kasance dan wasa da ya fi kowane dan wasa na kasar ta Jamus masu buga Firimiya lig a kasar Ingila zurara kwallaye a raga.
Dan wasan a yanzu haka ya jefa kwallaye dai-dai har guda 30 a wasanni daban-daban a gasar ta Firimiya.
Ozil mai shekaru 30 da haihuwa a duniya ya samu wannan nasarar da ya cika kwallaye 30 a raga a wasan da kungiyar ta Arsenal ta lallasa takwararta Leicester City da ci 3-1 a wasan na mako 11.
Ku Duba Wannan Ma Ana Rade-Radin Kocin Real Madrid Julen Zai "Kara Gaba"Dan wasan Ozil ya farke kwallo ta farko wa Arsenal a minti na 45 ana daf da tafiya hutun rabin lokaci, bayan da dan wasan Arsenal Bellerin, ya ci gida wato (Owngoal) a minti na 31 inda aka tafi hutun rabin lokaci ana 1-1.
Daga karshe aka tashi Arsenal ta doke Leicester da ci 3-1 wanda hakan ya kasance mata ta yi wasanni 10 kenan a jere tana samun nasara.
Ozil ya haura kan tsohon dan wasan kasar Jamus Jurgen Klinsmann, wanda ya zura kwallaye har 29 a yayin da yake buga wasa wa kulob din Tottenham na kasar Ingila tun daga shekara ta 1994 - 1995, 1997 har zuwa 1998.
Your browser doesn’t support HTML5